Jami’an DSS sun hana ma’aikatan hukumar EFCC shiga ofishinsu da ke Lagos

0
145

Rahotanni daga jihar Lagos a kudancin Najeriya na cewa jami’na tsaron farin kaya na DSS sun hana jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC shiga ginin shalkwatar Ofishinsu da ke unguwar Ikoyi a tsakar birnin jihar yau talata.

Babu dai cikakken bayani game da dalilin daukar wannan mataki na jami’an DSS wajen hana ma’aikatan na EFCC shiga ofishinsu, inda majiyoyi daban-daban ke tabbatar da cewa babu ko jami’I guda da ya samu damar aiwatar da aikinsa a hukumar yau.

A cewar EFCC wanna mataki na jami’an DSS ya tilasta dakatar da tarin shari’o’i da ake yiwa mutanen da ake tuhuma, haka zalika tarin masu laifi sun koma gida ba tare da samun damar yi musu tambayoyin kan tuhumar da ake musu ba.

Tsawon shekaru dai jami’an na DSS ke aiki a harabar ginin na EFCC amma ba a taba samun tsaiko ba sai a wannan lokaci.

Majiyoyin sun ce jami’an na DSS sun girke tarin motocin sulke a kan hanyar da za ta sada jami’an da ginin ofishin na EFCC wanda ya hana su iya ketarawa.

Rahotanni sun bayyana cewa halin da aka shiga baya rasa nasaba da takun sakar da bangarorin biyu ke yi game da hukumar da ta mallaki ginin wajen.

Kowanne bangare tsakanin hukumar ta EFCC da DSS na ci gaba da ikirarin mallakar ginin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here