Kano za ta sake bude shari’ar zargin kisan da ake yi wa Alhassan Doguwa – Abba gida-gida

0
126

Sabon Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a ranar Litinin ya sha alwashin sake bude shari’ar zargin kisan da ake yi wa shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa.

Idan dai za a iya tunawa dai a makon da ya gabata ne tsohon babban Lauyan jihar kuma kwamishinan shari’a na jihar, Musa Lawan ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta wanke Alhassan Ado Doguwa kan duk wasu tuhume-tuhumen da suka shafi kisan kai da kone-kone da ake yi masa.

A baya dai, an kama Alhassan Doguwa, tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da bayar da umarni da kuma hannu a cikin zargin kashe mutane kusan 15 da aka yi a zaben shugaban kasa/Majalisar Tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu a Tudun wada – daya daga cikin kananan hukumomin biyu na mazabar da yake wakilta a majalisar tarayya da suka hada da Doguwa/Tudunwada. Sai dai, Doguwa Ya musanta wannan zargi da kakkausar murya.

A jawabinsa na farko bayan rantsar da shi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce zai duba lamarin da kuma sauran laifukan zabe da aka tafka a cikin shekaru takwas na gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here