Sabon gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare, ya soki tsohon gwamnan Jihar Bello Matawalle kan barin asusun gwamnatin jihar ba tare da ko kwandala ba.
Ya yi wannan sukar ce, a dandalin baje koli da ke a garin Gusau jim kadan bayan an rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar.
Dare ya nanata cewa, bai iske ko kwandala daya ba, bayan ya karbi ragamar shugabancin jihar daga gun tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle.
A cewarsa, “Ina son in sanar da alummar jiharo0 Zamfara cewa, na gaji asusun gwamnatin jihar ba ko kwandala daya, na kuma gaji bashin dimbin biliyoyin Naira. ”
Ya roki alummar jihar da su kara hakuri su kuma bai wa gwamnatin sa goyon bayan su a cikin wannan halin da na iske jihar.
Dare ya yi alkwarin cika alkawaran da ya daukar masu a lokacin yakin neman zabe na neman kuri’unsu, mussaman bangaren samar da tsaro, ilimi, samar da ayyukan yi, kiwon lafiya da kuma habaka fannin aikin noma.
A cewarsa, “Da izinin Allah, na zo ne don na tsamo jihar daga halin da take ciki a yanzu, zan kuma iya kokari na wajen kai jihar ga tudun mun tsira.”
Leadership ta ruwaito cewa, hukumar EFCC ta ayyana Matawalle, a matsayin wanda take nema bisa zargin da badalar Naira biliyan 70.
Matawalle da kuma mataimakin sa, Hassan Nasiha, ba su halarci taron rantsar da Dare ba.
Matawalle ya jima da ficewa daga jihar tun bayan da ya fadi a zaben.