Sabon gwamnan Kano ya kori shugaban hukumar alhazai na jihar da wasu

0
134

Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya kori babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jiha, Muhammad Abba Danbatta.

Har ila yau, an sauke Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin shugaban hukumar. 

An bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, da aka fitar a safiyar Talata.

“Sakamakon haka, Gwamna Yusuf ya amince da nadin Alhaji Laminu Rabiu a matsayin sabon sakataren zartarwa na hukumar jin dadin alhazai ta jiha. Yayin da aka maye gurbin Sheikh Pakistan da Alhaji Yusuf Lawan a matsayin sabon shugaba.”

Daya daga cikin fitattun mutanen da sauyin ya shafa, akwai diyar marigayi, fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Jafar Mahmud Adam, Malama Nana Aisha.

Sabbin mambobin hukumar sune:  Sheikh Abbas Abubakar Daneji, Sheikh Shehi Shehi Maihula, Amb. Munir Lawan, Sheikh Isma’il Mangu, Hajia Aishatu Munir Matawalle, da Dr. Sani Ashir.

Sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran wadanda aka nada za su karbi ragamar tafiyar da harkokin hukumar nan take domin ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here