‘Ƴan sanda sun kama mutane 12 bisa zarginsu da laifuka daban-daban a Gombe

0
97

Rundunar yan sandan jihar Gombe ta gabatar da wasu mutane 12 ga manema labarai, wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.

Da yake karin haske ga manema labaran a hedkwatar rundunar, Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar, CP Okua Etim ta bakin Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ASP Sa’ad Sharif, yace “Rundunar ƴan sanda a Gombe ta samu nasarori da dama a cikin wannan mako, ta kama wassu da ake zargi da laifukan fashi da makami, da fyade, da sojan gona, da sata, da ƴan kulla makirci, da fasa gida da kwacen wayar salula da dai sauransu”.

Yace rundunar ta kama wani matashi mai suna Habu Muhammad Kabir, bisa zargin sa da yin sojan gona, inda ya je sansanin horas da mahajjata dake Kwalejin Horar da Malaman Arabiyya ta Gombe, ya kuma gabatar da kansa a matsayin ma’aikacin Hukumar Tattara Harajin Cikin Gida ta Jihar don ya damfari maniyyatan jihar da sunan karban kudin haraji.

Wadda ake zargin ya amsa laifin buga jabun katin shaida da rasiti da kuma hatimin hukumar, inda ya karbi kudi Naira 30,000 daga hannun wassu maniyata biyu.

Sharif yace rundunar ta kuma kama wassu da dama wadanda ake zargi da laifukan fyade da fashi da makami, da fasa gida, da hadin baki da kuma sata.

Ya ce a yayin kamen, ƴan sandan sun samu wassu kayayyaki da makamai da suka hada da takardun bogi, da kwamfyuta tafi-da-gidanka, da injin dab’i (printer), da katin shaida na jabu, da tsabar kudi, da dan kamfai da kyalle, da adduna, da wukake, da tarin guraye da layu, da wayoyin hannu da dai sauransu.

Jami’in hulda da jama’an na rundunar ƴan sandan ya ce bayan kammala bincike, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Da yake shawartar jama’a su rika baiwa jami’an tsaro bayanan da suka dace don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, jami’in ya ce rundunar ta himmatu wajen samar da zaman lafiya da tsaro ga al’ummar jihar.

Ya kara da cewa, rundunar ta samar da layukan waya na musamman don kai rahoton duk wata matsalar tsaro a jihar.

“Kuna iya kira a duk lokacin da kuka fuskanci aika-aika irin ta ƴan kalare ko wata matsala ta tsaro a gida ko a wurin aiki a faɗin Jihar Gombe, kar ku yi wata-wata, ku tuntubi lambobin mu na gaggawa 08150567771 ko kuma ku kira ƴan ‘Operation Hattara’ a kan 08035158691 ko kuma 09139962191”

Yayin zantawar su da manema labarai, wasu daga cikin wadanda ake zargin sun yi nadamar abin da suka aikata, suna masu bayyana hakan da cewa rudin shaidan ne.

Da suke rokon a yi musu sassauci, wadanda ake zargin sun bada tabbacin gyara halin su, tare da zamowa mutanen kwarai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here