Ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya za ta fara yajin aiki kan cire tallafin mai

0
82

Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ ta ce za ta bi sahun ƙungiyar Kwadago ta NLC a ƙasar wajen tsunduma yajin aiki daga ranar Laraba mai zuwa, saboda cire tallafin man fertur.

Ƙungiyar ta bayyana cikin wata takarda da ta fitar, bayan ganawar da kwamtin gudanarwarta ya yi da safiyar ranar Asabar domin tattauna batun cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi da kuma matakin ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ɗauka na shiga yajin aiki a tsakiyar makon da ke tafe.

Ƙungiyar ta NUJ ta ce a halin da ake ciki tashin farashin man fetur da na sauran kayayyaki sun jefa al’ummar ƙasar cikin mawuyacin hali.

Haka kuma ƙungiyar ta umarci mambobinta da ke faɗin jihohin ƙasar da su fara yajin aiki tare da fita zanga-zanga daga ranar Laraba 7 ga watan Yuni matuƙar kamfanin mai na ƙasar NNPCL bai janye ƙarin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here