Barcelona na gab da saye Gundogan, Arsenal ta daidaita da Rice

0
135

Kyeftin ɗin Manchester City Ilkay Gundogan na gab da komawa Barcelona idan kwantiraginsa ya kare a wannan kaka, inda kungiyar ta La Liga ke shirin gwangwaje ɗan wasan mai shekara 32 da kwantiragin shekara uku.(Sport – in Spanish)

Chelsea za ta buƙaci £35m kan ɗan wasanta na Croatia Mateo Kovacic, mai shekara 29, wanda Manchester City ke zawarci. (90min)

Arsenal ta amince da yarjejeniyar saye ɗan wasan West Ham Declan Rice, mai shekara 24. (FootballTransfers)

Amma Bayern Munich ba ta hakura ba da farautar Rice bayan wata ganawa da suka yi da shi a Landa, kungiyar ta Jamus na shirin gabatar da masa da tayi mai tsoka. (Sky Sport Germany)

Manchester United za ta gabatar da tayi kan Harry Maguire, mai shekara 30, zuwa ga Chelsea a matsayin wani ɓangare na daidaitawa da ɗan wasan Ingila Mason Mount, mai shekara 24. (Mirror)

Bayern da Manchester United na zawarcin ɗan wasan Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 23. (Nicolo Schira – in Italian)

Liverpool ta amince ta mutunta yarjejeniyar da aka cimma kan Alexis Mac Allister, sannan za ta biya Brighton tsakanin £55 zuwa 60m kan ɗan wasan asalin Argentina, mai shekara 24. (Football Insider)

Barcelona na da kwarin gwiwar cewa tsare-tsarensu na kuɗaɗe zai samu amincewar La Liga, hakan zai ba ta damar soma cinikin ‘yan wasa, ciki harda sake dawo da Lionel Messi daga Paris St-Germain. (90min)

Karim Benzema zai gana da Real Madrid kan kwantiraginsa da ke karewa, duk da cewa ana raɗe-raɗin zai karbi tayi mai gwaɓi da aka gabatar masa daga Saudiyya. (Marca)

Kungiyoyin Saudiyya sun shiga farautar ɗan wasan Sifaniya Sergio Ramos, mai shekara 37,wanda aka tabbatar zai bar PSG a wannan kaka. (Fabrizio Romano)

Shi ma ɗan wasan Chelsea da ba ta sabunta kwantiraginsa ba N’Golo Kante, ya samu tayi daga Saudiyya, sai dai kuma ɗan wasan mai shekara 32 na son tafiya PSG a Faransa. (90min)

Real Madrid ta kwaɗaitu da ɗan wasan Chelsea Kai Havertz mai shekara 23, kuma jami’ansa na tattauna kan komawarsa Jamus. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Mutumin da Manchester United ke hari Randal Kolo Muani ya gabatar da kansa ga Real Madrid. (Marca via Mail)

Everton na kokarin cimma yarjejeniya da ɗan wasan Ingila Tammy Abraham mai shekara 25, kan £27m. (Sun)

Ana sa ran ɗan wasan Ingila Reiss Nelson, mai shekara 23, ya sanya hannu a sabon kwantiragi da Arsenal.(Mail)

Sheffield United na nazari kan ɗan wasan Wolves Conor Coady, mai shekara 30.(Football Insider)

Steven Gerrard mai shekara 43 da Scott Parker mai shekara 42 na cikin jeren mutanen da ake ganin za su karɓi ragamar horar da Leeds United da West Bromwich Albion. (Telegraph – subscription required)

Leicester City na son dauko tsohon kocin Brighton da Chelsea Graham Potter.(Sun)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here