Nijeriya za ta so ta dauki matakan dakatar da fitar da zinare da ake yi ba bisa ka’ida ba daga kasar zuwa ketare, galibi ana hako zinaren ne ba bisa ka’ida ba kuma a fitar da shi ba bisa ka’ida ba daga yankunan da suke da dimbin arzikinsa a arewaci da kuma kudu maso yammacin kasar.
An samar da wurin gyarawa da sarrafa zinare a garin Mopa a jihar Kogi wadda ke tsakiyar kasar.
Wurin wanda aka kaddamar a kwanan nan ana saran zai taimaka wa kananan masu hako ma’adanai wajen gyarawa da sarrafa zinare a Nijeriya.
Ministan Ma’adanai da Tama Mai Barin Gado na Nijeriya Olamilekan Adegbite ya ce wurin zai taimaka wajen samar da tsari ga kananan masu hako ma’adanai da taimaka wa wajen magance matsalar ci da gumin masu hako ma’adanan.”
Babban burin shi ne a karfafa gwiwar matasa don su shigo “harkar gyarawa da sarrafa ma’adanai,” in ji shi lokacin kaddamar da wurin.
A wurin an tanadi injinan gyarawa da sarrafa zinare da sauransu. Har ila yau akwai rumfuna 30 da wurin bayar da horo da bangaren ofisoshi da bangaren samar da wutar lantarki da sauransu.
A wani yunkuri na rage hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, gwamnatin ta fara yi wa kananan masu hako ma’adanai rijista a duk fadin kasar.
“Yanzu haka muna samar da yanayin da zai takaita hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba da kuma yadda ake fasa kwaurinsa don samar wa gwamnatin kudin shiga da albarkatunsa da samar da ayyukan yi da sauransu,” in ji Adegbite.
Cin kudi da asarar rayuka
An shafe tsawon shekaru kananan masu hako ma’adanai suna hako zinare da sayar da shi babu tsari a fadin Nijeriya.
Ta irin wannan hanyar ce ake hako ma’adanai a gaba dayan yankin arewa maso yamma da yankin tsakiyar kasar da kuma yankin kudu maso yammacin kasar.
Duk da ribar da ake samu, irin wannan hanya ta hakar ma’adanai tana tattare da hadari ga kashe kudi da kuma asarar rayuka a wasu lokuta.
Daruruwan yara ne suka mutu sanadiyyar gubar dalma yayin hakar ma’adanai a jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin kasar tsakanin shekarar 2010 zuwa 2021.
Sai dai labari mai dadi dangane da matsalar gurbacewar ruwa da kasa da kuma abinci da aikin hakar ma’adanai ke jawowa saboda wasu mazauna yankin da taimakon wasu masu ruwa da tsaki na kasashen waje sun magance matsalar ta hanyar tsaftace yankin.
Sai dai akwai wani babban kalubale da ke ci gaba da ci wa Nijeriya tuwo a kwarya wato batun yadda ake fitar da dimbin zinare ba bisa ka’ida ba daga kasar zuwa ketare saboda wasu matsalolin tsare-tsare da dokoki.
Yadda ake kasuwancin zinaren ba bisa tsari ba yana jawo wa gwamnati rashin samun kudin shiga da kuma rashin ayyuka, a cewar ministan ma’adanan.
Daya daga cikin matakan da gwamnati ta dauka don magance matsalar shi ne wani da ta kafa mai suna Presidential Artisanal Gold Mining Development Initiative (PAGMDI), wanda zai rika sayan zinare kai-tsaye daga masu aikin hako ma’adanai.
An kaddamar da shirin ne a shekarar 2019. A shekarar 2020, kamar yadda Kungiyar masu kasuwancin zinare ta London Bullion Market Association ta bayyana an biya Babban Bankin Nijeriya (CBN) kudaden zinare da suka kai nauyin kilogram 12.5 ta hanyar wannan shiri.
Lokacin da aka samar da sinki-sinkin zinaren a shekarar 2020, tsohon Shugaba Buhari ya ce idan aka inganta harkar hakar ma’adanai a kasar za ta samar da ayyuka 250,000 yayin da kuma za ta samar da samar da kudin shigar da ya kai dala miliyan 500 na lasisi da kuma haraji ga gwamnati.
Zinare ya rasa haskensa
Kodayake nasarar da kamfanoni masu zaman kansu kamar Segilola Resources Operating Ltd suka samu a harkar hakar zinare ya ja hankalin masu zuba jari a ciki da wajen Nijeriya, galibi kananan masu hakar ma’adanai ne suka fi hako ma’adanai a Nijeriya, in ji ministan mai barin gado Adegbite.
Za a iya cewa hakan yana nufin yawancin masu harkar ma’adanai za su fahimci muhimmanci wurin gyarawa da sarrafa zinare a jihar Kogi.
Babban Masani kan Hakar Ma’adanai Abdullahi Lawal ya ce wurin zai taimaka wajen samar da zinare mai yawa wanda kananan masu hako ma’adanai ke hakowa.
Kara yawan zinaren da ake hakowa “zai kawo karin kudin shiga,” in ji shi. Wani babban kalubalen kuma shi ne yadda wurin gyara zinaren yake nesa daga wuraren da ke da arzikin zinare a yankin arewa maso yamma da kudu yammacin Nijeriya.
Masana suna ganin ya kamata hukumomi samar da hanyar da za a hada wuraren hakar ma’adanai da wurin gyara zinaren a duk fadin kasar.
Lawal ya ce ya kamata gwamnati ta samar da hanyoyin sufuri tsakanin wuraren da ake hako ma’adanai da wurin da ake gyara zinare a duk inda ake hako ma’adanai a fadin kasar.
Matsalar tsaro ta zame wa harkar hako ma’adanai kalubale a wasu bangare na kasar. Masana suna ganin idan ba a yi wani abu ba don magance matsalar, matsalar tsaro za ta kawo cikas ga ayyukan wurin gyarawa da sarrafa zinaren.
Idan aka samar da tsaro ana saran harkar hako zinare da gyara shi za su bunkasa a Nijeriya wanda hakan zai samar da ayyukan yi da kuma kudin shiga ga gwamnati.
A matsayinta na kasa da take kokarin rage dogaro da danyen man fetur da ake hakowa, Nijeriya za ta iya idan aka samu karin kudin shiga daga da ayyukan yi bayan gwamnati ta shiga harkar.