amince da korar jami’an cibiyoyi masu kula da harkokin Hajji a daukacin kananan hukumomi 44 na jihar.
Gwamnan ya kuma nada jami’an rikon kwarya da za su rika lura da yadda ake gudanar da ayyukan hajjin na shekarar 2023.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, babban sakataren yada labarai na gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya bayyana abubuwan da ake bukata jami’an wucin gadin da aka nada da su fara aiki cikin gaggawa don sauke alhakin da ke kansu.
Sanarwar ta kuma umurci sabbin jami’an cibiyar da aka nada da su yi gaggawar ganawa da babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano da aka nada kwanan nan domin gudanar da taron gaggawa a ranar Lahadi 4 ga watan Yuni 2023 a hedkwatar hukumar.
Wannan matakin na zuwa ne, a wani yunkuri na yin gyara da kuma daidaita harkokin tafiyar da al’amuran hukumar aikin Hajji a jihar wanda sabuwar gwamnatin jihar ta kuduri aniya.