Gwamnatin Kano ta yi tir da masu farwa kayan jama’a da sunan neman ganima

0
114

Gwamnatin Jihar Kano na sanar da al’ummar Jihar cewa ba za ta lamunci afka wa gine-ginen mutane da sunan cin ganima ba, a dukkan sassan jihar.

Haka kuma gwamnati na bayyana takaicin ta bisa yadda wasu Matasa suka afka wa ginin dake cikin tsohon gidan jaridar Triump da ke Fagge alhalin wannan ginin baya cikin lissafin wuraren da za a rushe.

Sabo da haka gwamnatin na ƙara jadadda cewar duk wanda aka samu da laifin afka wa wani gini tare da kwashe kayayyakin jikin sa zai gamu da fushin hukuma.

Gwamnatin ta ƙudiri aniyar yin aiki ne domin ci gaban Jihar Kano ba domin bai wa wasu lasisin rushe gine-gine da sace kayan mutane babu gaira babu dalili ba.

Wannan sanarwa ce da gargaÉ—i daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here