Kwamandan Hisbah Ibn Sina ya nemi afuwar jama’ar Kano

0
119

Shugaban Hukumar Hisbah na Jihar Kano da ke Nijeriya, Sheik Muhammad Haruna Ibn Sina ya nefi afuwar jama’ar Jihar Kano.

Ibn Sina ya yi wannan neman gafarar ne a wani taro da jami’an Hisbah a Kano a ranar Laraba.

A cikin jawabin da ya yi mai kama da bankwana, ya ce duk wanda ya yi wa laifi tsawon shekaru ukun da ya shafe yana jagorantar hukumar ya yafe masa.

“Cikin ‘yan kwanakin da suka rage, wadanda na batawa, ta iya yiwuwa a yanayi irin na aiki wani ya ga ba a yi masa daidai ba ko kuma kuskure ya sa na yi maka wani abu wanda na zalunce ka komin kankanta ba da sanina ba, ina neman afuwarku don Allah, ina neman alfarmar ku yafe mini,” in ji Ibn Sina.

“Ni dai duk abin da kuka yi mani tun daga kan abokan aiki zuwa ku kanana ina shaida muku cewa duk abin da kuka yi mini na yafe muku,” in ji Ibn Sina.

Sannan kuma ya gode wa gwamnan Jihar Kano mai barin gado Abdullahi Umar Ganduje kan irin taimakon da ya ba hukumar Hisbah. Ya bayyana cewa gwamnan Kano ya yi wa ‘yan Hisbah dinki kusan kala 20,000.

A jawabin da Ibn Sina din ya yi, ya kare wasu matakai da ya dauka a jihar musamman na lalata barasa inda ya ce sun lalata miliyoyin kwalaban barasa.

Ya bayyana cewa kwalaban da suka lalata na barasa sun tasar wa miliyan 10 tun daga fara aikinsa.

Sannan ya sake gode wa Allah kan damar da ya samu ta jagorantar wannan hukuma inda ya ce akwai lokacin da sama da mutum 37 da ke neman wannan kujera amma Allah ya dauko shi ya ba shi ita.

Ibn Sina kuma ya roki Allah ya sa wanda zai gaji kujerarsa ya zamo wanda ya fi shi kwarewa da kuma kawo ci gaba ga hukumar Hisbah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here