Yan bindiga sun kashe mutane 37 ta re da hana yi musu jana’iza a Sokoto

0
97

Kimanin mutane 37 aka bada rahoton mutuwar su, sannan wasu da dama suka jikkata a wasu hare-hare da aka kai kauyukan Raka da Raka Dutse da kuma Filin Gawa na karamar hukumar Tangaza a jahar Sokoto da ke Arewacin Najeriya.

A cewar wani ganau, da yammacin Asabar ne ‘yan bindigar suka kai hari garuruwan.

A lokacin da tsohon shugaban karamar hukumar Bashar Kalenjeni ke tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutane 18 aka kashe a Raka da 17 a Filin Gawa sai kuma mutum biyu a Raka Dutse.

Kalenjeni ya ce a daren Asabar din ne suka so yi musu sutura, amma sai dai ‘yan bindigar sun hana su har zuwa safiyar lahadin din nan ba’a suturta su ba.

A cewar sa, laifin da al’ummar da ke zaune a kauyukan suka yiwa ‘yan bindigar shine, rashin biyan harajin da suke dora musu.

Kalenjeni ya kara da cewar, suna jiran isowar jami’an tsaron da za su yi musu rakiya shiga kauyukan don gudanar da jana’izar mamatan.

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta ce kakakin rundunar ‘yan sandan jahar ASP Ahmad Rufa’I, ya ki cewa komai dangare da lamarin.

Jahar Sokoto na daya daga cikin jahohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga a shiyar Arewa maso Yammacin Najeriya, lamarin da kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da raunata wasu da kuma sanya wasu barin muhallan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here