Gasar kwallon kafar Saudiya na shirin karbar bakuncin Messi da Benzema

0
137

Wani lokaci a nan kusa ake sa ran tauraron Real Madrid  Karim Benzema da gwarzon dan wasan kungiyar PSG Lionel Messi su koma taka leda a gasar kwallon kafar Saudiya.

Wadannan bayanai sun fito ne jim kadan bayan da kungiyar Real Madrid ta tabbatar da shirin rabuwa da  dan wasan na ta na gaba, wanda ke rike da kyautar gwarzon dan kwalllon kafa na duniya ta Ballon d’Or.

A baya bayan nan ne dai tashar talabijin ta Al-Ekhbariya a Saudiyya ta yi ikirarin cewa Benzema mai shekaru 35 ya kulla yarjejeniya da kungiyar Al-Ittihad da ke birnin Jeddah.

Jimillar kwallaye 354 Benzema ya ci wa Real Madrid a wasanni 648 da  ya buga wa kungiyar, wadda ya kulla yarjejeniya da ita a ranar 9 ga  watan Yulin shekarar 2009.

A wani labarin kuma, rahotanni sun ce manyan jami’ai daga kungiyar Al Hilal sun yi tattaki zuwa Faransa don kokarin kulla yarjejeniya da Messi, bayan dan wasan mai shekaru 35 ya buga wasansa na karshe a Paris Saint-Germain a ranar Asabar.

Lionel Messi.
Lionel Messi. REUTERS – CHRISTIAN HARTMANN

Kafin karkare kakar wasa ta bana dai, Lionel Messi ya fuskanci tsangwama daga magoya bayann PSG a lokuta mabanbanta, sakamakon kayen ko rashin nasarar lashe wasannin da suke ganin ya kamata a ce dan wasan ya bayar da gudunmawa wajen samun nasara.

Sai dai fitattun ‘yan wasa da kuma masu sharhi kan kwallon kafa a ciki da wajen Faransa sun caccaki masu sukar Messi, wanda suka ce ya cancanci a girmama shi cikin kowane hali saboda kimarsa a duniyar kwallon kafa.

A tsawon shekaru biyu da ya shafe a PSG kwallaye 32 Messi ya ci wa kungiyar a cikin wasanni 75 da ya buga mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here