Osimhen ya kafa tarihin lashe takalmin Zinare da kofin Seria A a kaka guda

0
135

Victor Osimhen ya lashe kyautar takalmin zinare a Italiya, bayan da ya zama dan wasan da ya ci mafi yawan kwallaye a gasar Seria A.

Nasarar dai ta bashi damar kafa tarihin zama dan Afirka na farko da ya kai wannan mataki.

Karin tarihin da Osimhen ya kafa kuma shi ne zama dan wasa na farko da ya samu nasarar hade kyautar takalmin zinare da kuma lashe kofin gasar Seria A a lokaci guda, da ake kira da ‘Scudetto’ tun shekarar 2009, lokacin da Zlatan Ibrahimovic ya kafa nasa tarihin a kungiyar Inter Milan.

Kwallaye 25 Osimhen ya ci a kakar wasa ta bana, yayin da mai biye da shi Lautaro Martinez na Inter Milan ke da kwalllaye 21.

A halin yanzu Osimhen ne dan wasan Napoli na hudu da ya lashe kofin gasar Seria A da kuma kyautar cin mafi yawan kwallaye, inda ya bi sahun Diego Maradona, Edison Cavani, da Gonzalo Higuain.

Karo na farko Kenan da Napoli ta lashe gasar Seria A, cikin shekaru 33.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here