Majalisar wakilan Najeriya ta ce ƙaddamar da jirgin Nigeria Air ‘yaudara’ ce

0
103

Shugaban kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan harkokin sufurin jiragen sama, Nnolim Nnaji, ya ce kaddamar da kamfanin Najeriya Air da aka yi yaudara ce.

Ya bayyana hakan ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama wadanda suka ce ba su da masaniya kan kaddamar da jirgin.

Ministan sufurin jirgin sama a gwamnatin da ta gabata, Hadi Sirika ne ya ƙaddamar da jirgin a mako na ƙarshe na mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Sai dai lamarin ya haifar da ze-ce ku-ce kasancewar jirgin ɗaya ne tal aka bayyana a matsayin jirgin kamfanin, inda daga baya ake rinƙa raɗe-raɗin cewa jirgin ya yi ɓatan-dabo.

A nasu bangaren kuma kwamitin majalisar dattijan Najeriyar mai kula da harkokin sufurin jiragen sama ya soki kaddamar da kamfanin jirgin na Najeriya Air, inda ya ce lamarin wata rufa-rufa ce.

Mambobin kwamitin sun bayyana rashin jin dadinsu game da kaddamar da jirgin na kasa a wata ganawa da babban sakataren ma’aikatar sufurin jiragen sama, Emmanuel Meribole da babban darektan rikon kwarya na kamfanin Najeriya Air, kyaftin Dapo Olumide da kuma shugabannin hukumomin sufurin jiragen sama.

Da yake mayar da martani ga kwamitin, Kyaftin Dapo Olumide ya ce an kaddamar da jirgin ne a wannan lokacin domin a tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa lamarin ba karya ba ne.

Najeriya wadda ita ce ƙasa mafi yawan al’umma a Afirka ba ta da kamfanin jirgi mallakinta.

Wannan ne ya sanya gwamnatin da ta gabata ta yi yunƙurin samar da kamfanin jirgin wanda aka raɗa wa suna ‘Nigeria Air’, sai dai an gaza kammala tabbatar da yarjejeniyar bayan da wasu ƴan kasuwa a ɓangaren sufurin jiragen sama na Najeriyar suka shigar da ƙara a kotu suna ƙalubalantar tsarin da aka bi wajen kafa kamfanin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here