Angel Di Maria ya bar Juventus

0
131

Dan wasan tawagar Argentina, Angel Di Maria ya bar Juventus, bayan kaka daya da ya buga wa kungiyar tamaula.

Di Maria zai bar Italiya a matakin wanda yarjejeniyarsa ta kare a karshen kakar nan, wanda ake alakantashi da komawa Saudi Arabia.

Mai shekara 35, wanda ya lashe kofin duniya a Qatar tare da Argentina ya koma birnin Turin, bayan kaka bakwai da ya yi a Paris St Germain.

Di Maria ya ci wa Juventus kwallo takwas a wasa 40 da ya buga mata, kungiyar da ta kare kakar bana ba tare da daukar kofi ba.

Saudi Arabia ta ware fitattun ‘yan wasa 10 da take fatan dauka domin su koma buga gasar ta, wadanda ko dai sun lashe kofin duniya ko kuma sun dauki Champions League kamar yadda wata majiya ta sanar da AFP.

Cikin ‘yan kwallon har da Di Maria da dan wasan Real Madrid, Luka Modric da golan Tottenham, Hugo Lloris da kuma N’Golo Kante na Chelsea – dukkan ‘yan kwallon suna daf da yin ritaya.

Ranar Talata Karim Benzema ya saka hannu kan yarjejeniyar buga wa Al-Ittihad wasa, inda zai taka leda a gasar da Cristiano Ronaldo ke buga wa.

Ronaldo tsohon dan kwallon Real Madrid ya koma Al Nassr a cikin watan Janairu daga Manchester United, bayan kammala gasar kofin duniya a Qatar a 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here