Gwamnatin NNPP ta Kano ta wuce gona da iri – APC

0
112

Jam’iyyar APC mai adawa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yi Allah-wadai da matakin rushe gine-gine da sabuwar gwamnatin NNPP ta Abba Kabir ke yi jihar.

A wani taron manema labarai da jam’iyyar ta gudanar yau Talata, ta zargi gwamnatin Kanon da wuce gona da iri wajen daukar wannan mataki.

Mataimakin shugaban jam’iyyar Alhaji Shehu Maigari ya bukaci wadanda aka rusa wa kadaori su dauki matakan sharia domin kwato hakkokinsu.

Ya ce matakin gwamnatin Kanon ya sanya matasan jihar shiga harkar sace-sacen dukiyar Jama’a tare da lalata kadaori.

Rahotanni sun ce sabon gwamnan na Kano Abba Kabir Yusuf da kansa ya jagoranci rusa wasu gine-ginen da suka ce an yi su ba bisa kaida ba.

To sai dai Alhaji Shehu Maigari ya ce ba gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ce ta fara raba filaye a Kano ba,inda ya bukaci iyayen yara su gargadi yayansu kan kauce wa shiga ayyukan daba da sace-sace.

Sannan ya yi kira ga hukumomin tsaro a jihar su kara kaimi wajen sauke nauyin da ke kansu na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here