Lai Mohammed ya samu sabon mukami bayan ya bar gwamnatin Buhari

0
141

An nada tsohon ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed a matsayin babban abokin huldar kamfanin Ballard Partners, wani kamfani babban kamfani a duniya.

Hakan na zuwa ne kasa da mako biyu da rusa majalisar ministocin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

An tabbatar da saban mikamin na Lai Mohammed a cikin wata sanarwa da aka raba a shafin Ballard Partner na Twitter ranar Talata.

“Lai Mohammed, tsohon ministan yada labarai da al’adu na Najeriya, zai yi aiki a matsayin abokin gudanarwa na ofishin Abuja da ofishin tauraron dan adam na kamfanin a Legas, cibiyar hada-hadar kudi ta kasa.”

Shugaban kamfanin ya lura cewa an ba Mohammed mukamin ne saboda “yana daya daga cikin jami’ai da ake girmamawa a kasar”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here