‘Yan bindiga sun sace matar alkali a Adamawa

0
136

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Zainab Abbas, matar wani alkalin babbar kotu a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

‘Yansanda sun ce a ranar Laraba ne wadanda ake zargin suka je gidansu da ke unguwar Nyinbango a Jimeta a Yola da sanyin safiyar ranar kuma suka tafi da ita.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana lokacin da aka yi garkuwa da ita tsakanin karfe 1 na safe zuwa 2 na safiyar ranar Laraba.

Nguroje wanda ya fitar da sanarwa kan lamarin, ya bayar da tabbacin cewa rundunar ‘yansandan Jihar Adamawa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta ceto wanda lamarin ya shafa.

“Kwamishanan ‘yansanda, Afolabi Babatola, ya tura jami’ai domin aikin ceto. Jami’an za su gudanar da aikin ceto cikin dabara da basira,” in ji Nguroje.

Ya kara da cewa: “Za a tura sojoji da za su taimaka wajen ceto sa kuma yakar bata gari a Jihar nan.”

Jaridar Leadership Hausa ta rawaito cewa makonni biyu da suka gabata ne wasu ‘yan bindiga suka sace wasu fasto guda biyu daga yankin Nyinbango da ke Jimeta.

Fasto din da aka yi garkuwa da su sun tsira bayan wasu kwanaki bayan jami’an ‘yansanda sun yi artabu da wadanda suka sace su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here