Darajar takaddar kudi ta Naira ta sake yin mummunar faduwa a halastattun kasuwannin musayar kudaden ketare na Najeriya, inda farashin ya gangaro daga Naira 464.67 kan duk dala guda zuwa Naira 479.50 da kuma 469.50 a jiya alhamis.
Najeriyar Daily Trust ta fitar da rahoton cewa babban bankin kasar CBN ya karya darajar takardar kudin ta Naira a asirce batun da bankin ya musanta.
Rahotanni na nuna durkushewar hada-hada a kasuwannin musayar kudaden ketare na Najeriya tun bayan rantsar da sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Sabon shugaban Najeriya Bola Tinubu dai ya bukaci babban bankin na CBN ya samar da tsayayyen farashin a mabanbantan sassan canjin kudin da ke karkashinsa.