Gobara ta kone shaguna 30 a kasuwar Dubai da ke Damaturu

0
142

Akalla shaguna 30 ne wata gobarar dare ta kone a Kasuwar Dubai da ke bayan tasha a garin Damaturu ta jihar Yobe.

Ana dai zargin wutar lantarki ce ta yi sanadiyyar tashin gobarar tun daga daren ranar Alhamis har zuwa wayewar gari Juma’a.

Shugaban Kungiyar ’yan Kasuwar Yobe, Alhaji Usman Mu’azu ne ya bayyana hakan a yayin zantawarsa da wakilinmu a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.

Ya bayyana cewar, “gobarar ta tashi ne wajen karfe 1.00 na daren jiya wadda ta kai har wayewar gari yau ranar Jumu’ a tana dan ci nan da can duk da jami’an Hukumar Kashe Gobara sun yi ta kokarin kashe wutar.”

Alhaji Mu’azu ya ce wasu daga cikin mutanen da ke kusa da kasuwar ta Dubai sun bayyana masa hasashensu kan musabbabin tashin wannan gobara.

Ya ce wasunsu suna kyautata zaton ta tashi ne daga cikin wani shagon teloli da suka manta ba su kashe kayayyaki masu amfani da wutar lantarki ba bayan sun gama cin kasuwa.

Bayanai sun ce ana kyautata zaton dawo da wutar lantarki da aka yi cikin dare da karfi ne ya haddasa tashin gobarar.

Alhaji Usman Mu’azu ya tabbatar wa Aminiya cewar, ya zuwa yanzu akalla shaguna 30 ne dauke da kayayyaki na miliyoyin nairori suka kone kurmus da kuma wasu Gidajen kwana biyu na jama’a.

Da Aminiya ke tambayarsa kan ko akwai wani daukin gaggawa da Gwamnatin Jihar ta kawo wa wadanda wannan iftila’in ta shafa, ya ce ya zuwa yanzu dai bai ji wani abu makamancin haka ba sai dai kila nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here