Godwin Emefiele yana hannun mu — DSS

0
130

Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta ce yanzu haka Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele wanda shugaba Tinubu ya dakatar yana hannunta.

A safiyar yau Asabar DSS ta ce Emefiele ba ya hannunta a lokacin, kafin daga baya ta tabbatar da cewa ya shiga hannun nata a yanzu.

Tun a daren jiya Juma’a wasu rahotanni suka ce jami’an tsaron sun yi awon gaba da shi jim kadan bayan Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi daga mukaminsa.

“DSS na tabbatar da cewa Emefiele, tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, yanzu haka yana hannunmu don gudanar da bincike,” a cewar wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.

A gajeren sakon mai kalmomi bakwai da DSS ta wallafa a shafinta na Twitter bai bayyana cewa ko a ranar Juma’a Emefiele na hannunta ba, ballantana ta karyata cewa kwata-kwata ba ta tsare Emefiele ba.

Hakazalika akwai harshen damo da za a iya fahimtar sakin Emefiele hukunar ta yi kafin fitowar sanarwar.

Aminiya ta ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya dakatar da Emefiele nan take a ranar Juma’a sannan ya mika ragamar babban bankin ga mataimakin Emefiele, Folashadun Adebisi Shonubi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here