NIMET ta ankarar da ‘yan Najeriya game da barazanar ambaliyar ruwa

0
129

Hukumar kula da harkokin yanayi ta kasa a tarayyar Nigeria NIMET, ta ankarar da mazauna wasu jihohin arewacin kasar nan dangane da mamakon ruwan saman da ake sa-ran zubawa nan da ‘yan kwanaki masu zuwa. 

A cewar hukumar, wacce kan yi hasashen yadda yanayi zai kasance a kasar, tuni na’urorinta suka hango alamomin tsawa da walkiya a yankunan jihohin Borno, Taraba, Gombe, Bauchi da  kuma Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here