An kama mai bai wa ƴan bindiga bayanai da ƴan fashi 12 a Abuja

0
129

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Abuja babban birnin kasar ta kama wani da ake zargi da kwarmata bayanai ga masu masu garkuwa da mutane a Abuja.

Wanda ake zargin mai suna Mohammed Hamza dan shekara 25 wanda ake yi wa lakabi da Auta na daga cikin wadanda ‘yan sandan ke zargi da jigilar makamai ga ‘yan garkuwa da mutane da suka addabi birnin Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan reshen Abuja Josephine Adeh ta fitar, ta bayyana cewa Auta na daga cikin wadanda rundunar take nema ruwa a jallo.

“Wanda ake zargin na daga cikin wadanda rundunar ke nama, an kama shi saboda hannu a jigilar makamai da harsasai da kayan abinci da muggan kwayoyi ga masu laifi a maboyarsu daban-daban da ke cikin daji ta hanyar amfani da babur.

“Kayayyakin da aka gano daga wanda ake zargin sun hada da bindigar AK47 daya sai harsasan AK47 sai wayar salula daya da kayayyakin abinci da wani babur kirar Boxer da ba a yi wa rajista ba,” in ji sanarwar.

Haka kuma rundunar ‘yan sandan ta ce ta kama wasu mutum 12 wadanda ake zargi da kera bindigogi manya da kanana da fashi da makami da wasu laifuka.

Wadanda ake zargin suna hada da Daniel William mai shekara 51 sai Mohammed Yusuf mai shekara 41 da Abdulrasheed Abdullahi mai shekara 26 da Aminu Mohammed dan shekara 41 inda duka aka kama su a yankin Zuba da ke Abuja.

Haka kuma rundunar ‘yan sandan ta ce ta kama sauran mutum takwas din a wani wurin sayar da Amala a unguwar Utako inda har aka samu bindigogi guda uku a wurinsu da wukake da miyagun kwayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here