Fasinjoji 10 sun mutu a kan hanyar dawowa daga ɗaurin aure

0
117

Aƙalla mutum goma ne suka mutu, ƙarin wasu 25 kuma suka ji raunuka bayan wata motar bas ta yi karo a wani yankin da ya shahara kan harkar barasa a ƙasar Ostireliya.

Fasinjojin na dawowa ne daga wani ɗaurin aure a wani kamfanin sarrafa barasa cikin daren Lahadi a Hunter Valley, wani fitaccen wuri na masu yawon buɗe ido da ke zuwa shan barasa, lokacin da motarsu ta kife.

‘Yan sanda sun tuhumi direban motar bas ɗin mai shekara 58 a kan zarge-zarge guda goma masu alaƙa da mugun gudun da ya yi sanadin mutuwa.

Sun ce har yanzu suna ƙoƙarin tantance su wane ne mutanen da suka mutu.

Sai dai an ba da rahoton cewa ma’auratan ba sa cikin motar bas ɗin lokacin da hatsarin ya faru.

Kwamishiniyar ‘yan sanda Karen Webb ta ce wurin da aka yi karon “har yanzu ana yi masa kallon cikakken wurin da aka aikata laifi”.

Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 lokacin da a cewar ‘yan sanda ake zabga tururin saukar ruwan sama a yankin. Motar dai ta hantsila a lokacin da take ƙoƙarin juyawa a wani shataletale.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here