Janye tallafin mai: Masu kayan gwari sun koka kan rashin ciniki a Legas

0
122

Tun bayan da shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur kacokan a ranar da aka rantsar da shi, farashin man ya sauya daga Naira 185 zuwa 488 a mafi karancin farashi da ake sayarwa a jihar Legas, lamarin da ya janyo karancin man tare da cunkoson masu saye a akasarin gidajen mai.

Kodayake har zuwa lokacin hada wannan rahoto ana ci gaba da samun cunkoson masu sayen man fetur a gidajen man da ke sayar da lita a kan Naira 488 a Legas yayin da wasu gidajen mai suke a rufe.

Janye tallafin man ya shafi harkoki da dama, kamar sufuri da kayan masarufi, lamarin da ya sa ’yan kasuwa suke kokawa bisa tsadar sufuri da kuma rashin ciniki.

Aminiya ta ziyarci kasuwar kayan gwari ta kasa da kasa da ke mil 12 a Legas, inda ’yan kasuwar suke kokawa da rashin kasuwa da hauhawar farashin wasu daga cikin kayayyakin da suke sayarwa, tun bayan sanar da janye tallafin man.

Alhaji Aminu Musa shi ne shugaban bangaren ’yan tattasai na kasuwar ta mil 12, ya shaida wa Aminiya cewa a duk lokacin da aka samu karin farashin man fetur kusan komai ma farashinsa yana karuwa, kuma haka su ma abin yake a kasuwarsu.

Ya ce karin farashin man fetur na yanzu yana zuwa ne a lokacin da ake fama da karancin samun kudi domin ba a dade da farfadowa daga matsalar rashin takardun kudi ba, matsalar da ta tagayyara ’yan kasuwa tare da kassara harkokinsu.

Ya ce, “wannan karin farashin man a yanzu ya dada dagula al’amura domin ya janyo karancin kayan a kasuwa da hauhawar farashinsu da kuma karancin masu sayen su, domin kayan da a baya ake sayarwa Naira dubu biyar a yanzu sun koma dubu goma zuwa sha biyu, kuma idan a baya ana sauke mana kaya mota 70 zuwa 100, a yanzu ba a wuce 30 zuwa 25, domin idan dan kasuwa ya lissafa kudin da za a sayi mai, a yi dakon kayan, sai ka ga an hakura da kawo kayan domin ba za a fita ba.

“Haka kuma, baya ga wannan matsala a yanzu lokaci ne na karancin kayan gwari, saboda shigowar damuna.

“Ka ga abin zai hade mana biyu, ga karancin kaya ga tsadar man fetur. Fatan mu shi ne a samu maslaha tsakanin gwamnati da masu sayar da man fetur domin talaka ya samu sa’ida.”

Malam Ibrahim Dauda, dillali ne na tattasai a kasuwar mil 12 ya shaida wa Aminiya cewa, farashin tattasan ya haura duba da tsadar kudin dakon kayan da ake yi daga Arewa zuwa Legas, inda ya ce, a baya kudin motar da suke dauko kayan ba ya wuce Naira dubu 140, amma yanzu ya kai Naira dubu 250 kuma hakan ya yi tasiri sosai wajen tsadar kayayyakin.

Haka ita ma Blessing da ke zuwa kasuwar mil 12 domin sarar kayan gwari tana sayarwa ta shaida wa Aminiya cewa, a ‘yan kwanakin nan farashin kayan da take saye sun haura sosai ta yadda ko ta sayi kayan ta sayar ba ta samun riba, “ domin a baya kayan da muke saye daga Naira dubu 5 zuwa 6, su muke saya Naira dubu 22.

Ko a jiya da na sayi kayan ban iya mayar da kudin ba, sai asara ce ta biyo ni. Wannan shi ne halin da muke ciki.

Haka kuma wannan shi ne dalilin da ya sa da yawa daga cikinmu ba sa zuwa su sayi kayan, domin idan ka zo ka saya asara ce ke biyowa baya.

Fatanmu shi ne mahukunta su yi duba da wannan lamari domin abin da al’umma za su ci yana gaba da komai”. In ji ta.

Shi ko Malam Abubakar da ke sayar da tumatir a kasuwar mil 12 cewa ya yi, a bangaren ’yan tumatir matsalar da ’yan kasuwar ke fama da ita ce rashin ciniki, domin a baya ana sayar da kwandon tumatir Naira dubu 50 zuwa 55, amma a yanzu baya wuce Naira dubu 30 zuwa 40, sai dai duk da haka masu sayen kayan sun yi karanci saboda tsadar kudin motar da ke hadahada da su a cikin gari, “domin a baya masu sayen kayanmu za su biya kudin dakon tumatur Naira 500 zuwa 1000 a mota, a yanzu sai sun biya 2000 saboda tsadar mai.

“Wannan ne ya sa yawancin masu sayen kayan suka janye daga kasuwar.

“Hakazalika, yanayin yadda ake kawo kayan ma ya ragu sosai duk sakamakon janye tallafin man fetur”, in ji shi.

Alhaji Sulaiman Dan Adawa shi ne Sakatare na ’yan Kasuwar mil 12 a bangaren ’yan tumatir ya shaida wa Aminiya cewa, a baya kwandon tumatir ya yi tsada sosai a kasuwar, inda ya kai har Naira dubu 70 domin a wancan lokacin ana kawo tumatirin ne daga Arewacin Najeriya kadai, amma a yanzu lokacin samun tumatir daga sassa da dama da suka hada da yankin Yarbawa da ma kasashen Kamaru da Benin ya yi.

Don haka aka samu saukin farashin tumatir din, kodayake a yanzu an samu tsadar farashin man fetur, amma hakan bai sa tumatirin ya yi tsada ba kamar lokacin da ya yi a baya, “wannan abu ne na lokaci sai dai mu yi addu’a Allah Ya taimake mu domin tsadar man fetur dole ce taa shafi kowa saboda farashin sufuri dole ne ya tashi.

“Yanzu haka mu a kasuwarmu muna fama da karancin masu saye, rashin kasuwa shi ke damun mu, amma abu mafi muhimmanci shi ne mu ci gaba da addu’a”, in ji shi.

Shi kuwa Malam Abdullahi da ke sayar da kayan kanshi a kasuwar ta mil 12 cewa ya yi, a bangarensu na masu hada-hadar kayan kanshi da suka hadar da citta da tafarnuwa da kanumfari da sauran kayayyakin masarufi, janye tallafin man fetur bai shafi sana’arsu ba, domin mafi akasarin kayayyakinsu da manyan motocin daukar kaya ake dakon su daga Arewa zuwa Legas, kuma su manyan motocin suna amfani ne da disil ba fetur ba.

Shi man dizel dama tuni aka cire tallafin a kansa, don haka cire tallafin baya-bayan nan bai shafi farashin kayansu ba, domin a haka akwai kayan da farashin nasu ma raguwa ya yi sakamakon rangwamen da suka samu daga inda suke saro kayan daga Arewa, “Ni kiran da zan yi wa ’yan kasuwa shi ne, kada mu kara farashi a kan kayan da karin man fetur bai shafe su ba, domin manyan motoci ba fetur suke amfani da shi ba. Idan aka samu adalci a tsakanin ’yan kasuwa to talaka zai samu sauki”, inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here