Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin ba da rancen kudi ga daliban Najeriya

0
123

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya rattaba hannu a kan kudirin ba da lamuni ga dalibai, domin cika daya daga cikin alkawuran da ya dauka na samar da ‘yancin walwala a fannin ilimi a Nijeriya.

Tawagar kafafen yada labarai na shugaban kasa, karkashin jagorancin Mista Dele Alake, ne suka bayyanawa manema labarai a yau Litinin.

A cewar Alake wanda ya samu rakiyar wasu ‘Yan jaridu da suka hada da Tunde Rahman da Abdulaziz Abdulaziz da babban sakataren ma’aikatar ilimi David Adejoh, sabuwar dokar na daya daga cikin alkawuran zabe da shugaban kasa, Tinubu ya yi.

Da aka tambaye shin baya ganin sabuwar dokar ba za ta sanya hauhawar karin kudin makaranta ba, Alake ya ce dukkan al’amura biyun ba su da alaka, inda ya ce manufar dokar ita ce a taimaka wa dalibai marasa galihu su samu damar samun ilimi a Nijeriya.

“Muna matukar farin cikin sanar da ku cewa, a yau shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu a kan dokar ba da lamuni ga dalibai.

“Wannan shi ne alkawarin da dan takarar shugaban kasa a wancan lokacin, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa, na cewa zai ana bayar da rance ga dalibai, yanzu ya sanya hannu a kai. wannan kudurin doka daga yanzu zai ba wa dalibanmu marasa galihu damar samun lamuni na gwamnatin tarayya don biyan bukatunsu na neman ilimi ko sana’arsu kamar yadda ake haka a sauran kasashe da suka ci gaba a duk fadin duniya,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here