Yaushe ne za a ce namiji ya tsufa da haihuwa?

0
135

Akwai alamun cewa ubanni sun fara tsufa. Wani lokaci ma tsufa sosai.

Cikin kwanakin nan wakilan shahararren dan fim Al Pacino mai shekaru 83 da haihuwa suka tabbatar da cewa yana sa ran haihuwa da budurwarsa mai shekara 29, Noor Alfallah.

Amma ba shi kadai ba ne, abokin aikinsa Robert De Niro mai shekara 79 shi ma ya tabbatar da cewa ya na sa ran haifar dan sa na bakwai.

Wadannan mutanen biyu ba su kadai ba ne wadanda suka haihu suna da wadannan shekarun ba, wasu maza ‘yan fim da dama da mawaka har ma da shugabannin kasan Amurka sun haihu a lokacin da su ka tsufa.

Kuma matsakaicin shekarun sabbin masu haihuwa yana ta karuwa cikin shekarun nan.

Tsakanin shekarun 1972 da 2015, ya karu da shekara 3.5: Uba mai matsakaicin shekaru a Amurka ya na da shekaru 30.9, kuma kashi 9 a cikin su na da shekaru 40 a lokacin da suka haihu karon farko.

Mutumin da ya fi kowa tsufa da ya haihu a cewar ‘Guinness World Records’ na da shekara 92- duk da cewa akwai rade-radin cewa akwai wadanda suka fi shi tsufa da suka haihu.

Har ila yau zama uba a lokacin da mutum ya tsufa na tattare da wasu hadura.

A watan disamban 2022, masu bincike daga jami’ar Utah da sauran cibiyoyi sun wallafa wani bincike kan shekarun haihuwa da kuma yadda ya jibanci yanayin daukan ciki da kuma lafiyan jarirai.

Yayin da bincike da dama za su hada da masu shekaru irin na Pacino, soboda yadda ba su da yawa, akwai hujjoji da ke nuna cewa maniyin mazan da ke da shekaru arba’in zuwa hamsin yana da karancin inganci idan aka duba yawansa da sauran sinadarai.

Wadannan canje-canjen na nufin ana alakanta shekarun haihuwa da rashin iya daukar ciki da kuma samun barin cikin bayan an dauka, a cewar ma su bincike.

Bincike da dama ya nuna cewa hadarin samun barin ciki ya fi yawa idan uban na da shekaru.

Sai kuma akwai hadarin kamuwa da cuta bayan haihuwa. Ana sane tun shekarun 1950 cewa tsofaffin ubanni suna iya samun yara masu cutar ‘achondroplasia’.

Amma tun daga wannan lokacin, an sami bullowar wadansu cututtuka da za a jingina da hakan.

”An gano da gaske cewa shekarun uba na da irin alakar da shekarun uwa ke da shi da lafiyar ‘ya’ya”. A cewar masu binciken Uttah.

Masu bincike a jami’ar Stanford, misali, sun gano cewa za a alakanta shekarun uba da rashin nauyin sabbin jarirai.

Shekarun uba har ila yau na da dangantaka da wadansu nau’o’in cutar daji da ke bayyana a jarirai har ma da cututtukan zuciya.

Yana da kyau a tuna da cewa , duk da haka, kamar mafi yawan binciken da ke nazarin dangantaka tsakanin lafiya abubuwan da ke haddsa rashin sa ba su da tabbas.

Za a iya samun wasu abubuwa wadanda ke taka muhimmiyar rawa, kamar salon rayuwar iyaye da gurbacewar muhalli.

Duk da haka, masu bincike sun gano cewa yayin da maza suka tsufa, za su iya kamuwa da sauyin yanayin kwayoyin halitta da ‘ya’yansu za su iya gada.

Bincike irin wadannan na kawo canje-canje kan yadda likitoci da masu bincike ke tunanin kan yanayin daukar ciki.

Tarihi ya nuna cewa galibi a kan tuhumi shekarun mace ne idan har ana samun matsala wurin daukar ciki.

Tabbasa mafi yawan binciken sun karkata ne kan mata. Amma yanzu an fara gane cewa duk da ya ke mata sun fi maza saurin kaiwa matakin rashin haihuwa, shekarun namijin na da matukar muhimmanci.

A yanzu, batun Pacino da De Niro – da wasu maza da suka kai shekaru saba’in ko tamanin ko casa’in – sun kasance ba su da yawa.

Amma yanzu zama uba ba harkan samari ba ne kadai. Tun daga shekarun 1970, yawan ubanni a Amurka da ke da shekaru kasa da 30 ya ragu da kashi 27%, yayin da adadin ubanni masu shekaru 45-49 ya karu da kashi 52%.

Idan lamarin ya ci gaba a haka, dole fannin lafiya – da sauran halayen zamantakewa su sauya tunaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here