An kashe mutum 21 a wani sabon hari a Filato

0
88

Akalla mutum 21 ne suka mutu ciki har da wani limamin coci yayin da wasu da dama suka jikkata a daren Lahadi a kauyukan Rim da Jol da Kwi na Karamar Hukumar Riyom da Gana-Ropp a Karamar Hukumar Barkin Ladi.

Lamarin na baya-bayan nan na zuwa ne sa’o’i bayan da aka harbe wasu makiyaya biyu a unguwar Fas da ke Karamar Hukumar Riyom da yammacin ranar Lahadi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa jami’an tsaro na bincike.

Rundunar ‘yan sandan ta ce “An kashe Fulanin biyu ne yayin da aka kai harin cikin dare.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ziyarci wurin da lamarin ya faru. Ya ce “Muna kan binciken musabbabin harin.”

Aminiya ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun mamaye kauyukan ne a lokacin da mazauna yankunan da lamarin ya shafa ke tsaka da barci.

Rwang Tengwong, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Matasan Berom, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin ya bayyana cewa, “An kashe mutum biyu a kauyen Rim na Karamar Hukumar Riyom, an kashe mutum bakwai a Jol, 11 a Kwi yayin da kuma aka kashe wani limamin coci mai suna Rabaran Nichodemus Kim a Gana a Karamar Hukumar Barkin Ladi.”

Kungiyar YBM ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da jiha da su bullo da sabbin dabarun magance matsalar tsaro a kasar nan musamman a Jihar Filato.

A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Filato, Barista Caleb Manasseh Mutfwang, ya amince da nadin Birgediya Janar Gakji Goshwe Shipi (ritaya) a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin tsaron cikin gida.

Aminiya ta ruwaito cewa, jihar ta shafe fiye da shekara 20 tana fama da rikice-rikicen kabilanci da addini, inda aka kashe daruruwan mutane.

A kwanakin baya an kashe fiye da mutum 150 a kauyukan Karamar Hukumar Mangu da suka hada da mata da kananan yara.

Janar Shipi, har zuwa lokacin da aka nada shi, yana koyar da harkokin tsaro da dabaru a Kwalejin Yakin Soja da ke Abuja.

Sanarwar da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na gwamnan Gyang Bere ya fitar ta ce ana sa ran mai ba da shawarar kan harkokin tsaro zai nuna kwarewarsa wajen gudanar da sabon aikin nasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here