Kundin adana tarihi na Guinness ya tabbatar da bajintar Hilda Baci

0
176

Kundin Adana Tarihi na Duniya wato Guinness World Records, ya tabbatar da ’yar Najeriya, Hilda Effiong Bassey a matsayin wadda ta kafa tarihi wajen shafe tsawon lokaci tana girki.

Masu kula da kundin ne suka tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Talata.

Sun ce “Bayan cikakken nazari kan dukkan shaidu, a halin yanzu Kundin Tarihin na Guinness na iya tabbatar da cewa Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci, ta karya tarihin shafe tsawon lokaci inda ta yi sa’a 93 da minti 11 tana girki.”

Hilda mai shekara 27 ta fara girkin ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Mayun 2023, kuma ta ci gaba har zuwa ranar Litinin 15 ga watan Mayu.

Ta girka abinci iri daban-daban har fiye da 100 a tsawon kwana hudu.

Hilda dai ta yi yunkurin kafa tarihin shafe tsawon sa’a 100 tana girki ne ba tare da katsewa ba, amma sai masu kula da kundin tarihin suka cire kusan sa’a bakwai a lissafin da ta yi saboda kuskuren kidaya a lokacin gajeren hutu da ta rika yi.

Hilda ta karya tarihin Lata Tondon, ’yar Indiya wadda ta shafe sa’a 87 da minti 45 tana dafa abinci ba tare da katsewa ba.

A martanin da Hilda ta yi, ta ce wannan shi ne abu mafi soyuwa da ya taba samunta a rayuwa.

A cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce “wannan shi ne labari mafi soyuwa da na taba ji a rayuwata. Wayyo Allah, Wayyo Allah, Wayyo Allah, Na gode.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here