Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta fara tunanin sayar da Kylian Mbappe a wannan kaka saboda kaucewa asarar rabuwa da shi a kyauta cikin shekara mai zuwa, bayan da dan wasan ya tabbatarwa kungiyar cewa ba shi da shirin tsawaita kwantiraginsa.
A karshen shekara mai zuwa ne kwarantiragin matashin Bafaranshen zai kawo karshe duk da cewa akwai zabin tsawaitawa idan ya so, amma Mbappe mai shekaru 24 ya bayyana cewa yana fatan taka leda a wani lig na daban sabanin na kasar tasa.
Duk da sanar da matsayar dan wasan, PSG ta bashi dama daga yanzu har zuwa ranar 31 ga watan Yuli don ya yi tunani ko zai amince da bukatar tsawaita kwantiragin zuwa nan da shekarar 2025.
Idan har PSG ba ta mayar da hankali wajen cinikin Mbappe ba kenan dan wasan na da damar barin kungiyar a kyauta idan har kwantiraginsa ya kare, wanda ke nuna dole ta fara tattaunawa da tarin kungiyoyin da ke zawarcin zakakurin dan wasan mafi zura kwallo ga zakarar ta Lig 1.
PSG dai ta fusata matuka kan yadda wasikar da Mbappe ya aike mata game da kin yarda da tsawaita kwantiragin nasa ta watsu a dandalin sada zumunta.
A shekarar 2017 ne tauraron na Faransa da ya lashe kofin Duniya a 2018 ya kulla kwantiragi da PSG a matsayin aro daga Monaco gabanin sayenshi baki daya kan yuro miliyan 180 kuma daga lokacin zuwa yanzu ya zurawa kungiyar kwallaye 212 a wasanni 260 da ya doka.
A bangaren kasar shi Mbappe ya zurawa Faransa kwallaye 38 a wasanni 68 da ya doka ciki har da kwallaye 3 rigis da ya zura a ragar Argentina yayin wasan karshe na gasar cin kofin Duniya a Qatar.
Manyan kungiyoyin Turai da dama na harin Mbappe a yanzu haka ciki kuwa har da Real Madrid wadda ta so kai matashin Bernabeu a kakar da ta gabata amma ya zabi zaman shi a PSG.
Sai dai ana ganin tafiyar Karim Benzema dama ce ga Mbappe lura da yadda kungiyar ke lalubon sitireka duk da cewa ta na tattaunawa da Tottenham don kulla kwantiragi da Harry Kane.