PSG na duba yiwuwar sayar da Mbappe kafin kwantiraginsa ya kare

0
119

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain da ke buga gasar Ligue 1 ta kasar Faransa, na duba yiwuwar sayar da tauraron dan wasanta, Kylian Mbappe a bana domin guje wa rasa shi a badi inda kwantiraginsa zai kare.

Mbappe ya aike wa PSG wakisar cewar ba zai kara rattaba hannu kan wani sabon kwantiragi ba, hakan ya sa kungiyar ke shawarar rabuwa da shi tun yanzu don gujewa rasa shi a kyuata yayin da kwantiraginsa ya kare a karshen kakar badi.

Real Madrid ta nuna sha’awar daukar dan wasan amma ya watsa mata kasa a ido, amma barin kungiyar da Karim Benzema ya yi ka iya kara janyo hankalin kungiyar wajen neman Mbappe.

Kylian Mbappe wanda ya zo PSG a matsayin aro kafin su saye shi daga Monaco a kan kudi Yuro miliyan 180 ya zura kwallaye 212 a wasanni 260 da ya buga, kuma ya jefawa kasarsa Faransa kwallaye 38 a wasanni 68 ciki har da kwallo uku rigis da ya jefa a wasan karshe na gasar kofin duniya da suka buga da kasar Ajantina.

Mbappe ka iya zama shahararren dan wasa na biyu da zai bar kungiyar a bana bayan da Lionel Messi ya yanke shawarar barin kungiyar a bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here