A tattaunawar har da Ganduje da Uzodinma
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yanzu haka yana ganawa sabon Shugaban Majalisar Dattajai, Godswill Akpabio, a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja.
Kazalika, cikin tattaunawar akwai Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma da tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Shi ma Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu na tare da su a tattaunawar.
Gabanin haka, Shugaba Tinubu ya kuma gana da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a ofishinsa.
Sai dai har yanzu babu cikakken bayani game da makasudin duka ganawar tasu.
Shi ma shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya gana da Tinubun.