Yadda wata mata ta ‘mutu’ ta farfaɗo lokacin jana’izarta

0
95

Masu makoki a lokacin jana’izar wata tsohuwa ƴar kasar Ecuador sun firgita a lokacin da suka fahimci cewa matar tana da alamun rai.

A makon da ya gabata ne likitoci suka ayyana cewa Bella Montoya, mai shekara 76, ta rasu bayan da ta gamu da cutar da ake kyautata zaton ta bugun jini ce.

Bayan sa’a biyar ana cikin makoki da jana’izarta ranar Juma’a sai iyalai da sauran ƴan uwanta da ke shirin sauya mata kaya kafin a je a binne ta sai suka ga tana kokarin numfashi.

A yanzu dai an mayar da Ms Montoya asibiti inda aka kai ta sashen bayar da kulawar gaggawa, kuma ma’aikatar lafiya ta Ecuador ta sa a gudanar da bincike kan lamarin.

A wata sanarwa ma’aikatar lafiyar ta ce, matar ta fada yanayi na rashin numfashi ne da kuma tsayawar zuciya – kuma duk kokarin da aka yi na farfado da ita ya ci tura a lokacin, daga nan ne likitan da ke bakin aiki ya ayyana cewa ta rasu.

Kafofin yada labarai na kasar sun ruwaito dan matar, Gilber Rodolfo Balberán Montoya, na cewa an kai mahaifiyar tasa asibiti ne da wajen karfe tara na safe amma zuwa kusan 12 na rana sai likita ya ce masa ta rasu.

Daga nane ne aka sa Ms Montoya a akwatin gawa tsawon sa’o’i, sai kawai danginta suka lura tana neman yin numfashi.

An sanya hoton bidiyonta kwance a cikin budadden akwatin gawa, tana numfashi sama-sama, mutane da dama sun kewaye ta.

Sai kuma aka ga jami’an lafiya sun hallara suka dudduba ta kafin su fitar da ita daga cikin akwatin suka dauke ta zuwa motar asibiti.

Yanzu dai tana bangaren masu fama da tsananin rashin lafiya da ke bukatar kulawa sosai a asibitin da aka ayyana cewa ta mutu.

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito dan nata, Mr Balberán na cewa, ”sannu a hankali na fara fahimtar abin da ya faru. Yanzu ina addu’ar mahaifiyata ta samu lafiya. Ina fatan ganinta a kusa da ni.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here