Gbajabiamila ya yi murabus daga wakilcin mazabarsa a majalisar wakilai

0
138

Sabon Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen ya maye gurbin magabacinsa, Femi Gbajabiamila, wanda ya yi murabus.

An sanar da murabus din da Gbajabiamila ya yi daga majalisar ne a zauren a ranar Laraba.

Shugaban majalisar ya karanta wasikar da tsohon shugaban majalisar ya aike, inda ya bayyana aniyarsa na yin murabus.

A baya-bayan nan shugaba Bola Tinubu, ya nada Gbajabiamila shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya.

A ranar Talata ne aka zabi sabbin shugabannin za su jagoranci majalisar wakilai ta 10, inda Abbas Tajuddeen ya zama sabon shugabanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here