Real Madrid ta kammala ɗaukar Bellingham tsawon shekara shida

0
96

Real Madrid ta kammala ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Ingila Jude Bellingham daga ƙungiyar Borussia Dortmund a kan kwanturagin shekara shida.

Katafaren kulob ɗin na ƙasar Sifaniya zai biya yuro miliyan 103 don sayen ɗan wasan mai shekara 19, baya ga yiwuwar ƙarin wasu kashe-kashen kuɗi a kai.

Idan aka haɗa duka lissafin ƙarin kuɗaɗen, kwanturagin na iya kai wa har yuro miliyan 133.9.

A ranar Alhamis ne za a gabatar da Bellingham, wanda ya fara sana’arsa ta buga ƙwallo a Birmingham City, a matsayin ɗan wasan Real Madrid yayin wani biki na musamman.

“Ina gode wa kowa a BVB [Dortmund] da kuma masu sha’awar ƙwallon ƙafa saboda dukkan goyon bayansu a tsawon shekara uku da ta wuce,” a cewar Bellingham.

“Wata karramawa ce gare ni sanya jesinsu a tsawon lokaci da yawa.

“Duk da yake ina zuba ido ga inda zan kasance a nan gaba, amma ba zan taɓa mance zuwa nan ba. Ɗan Borussia, ba ya taɓa canzawa. Ina yi muku fatan alheri.”

An bayyana Bellingham wanda ɗaya ne cikin ‘yan wasan Ingila mafi ƙwazo a Gasar Cin Kofin Duniya ta bara, a matsayin gwarzon ɗan ƙwallo a Gasar Bundesliga ta kakar nan, yayin da Dortmund ya ɓaras da damar ɗaukar gasar karon farko a cikin shekara 11.

Kuɗin kafin alƙalamin da aka biya na nufin shi ne ɗan ƙwallon Ingila na biyu mafi tsada da aka saya bayan Jack Grealish, wanda kulob ɗin Manchester City ta saya daga Aston Villa a kan kuɗi fam miliyan 100 a 2021.

  • 2023

Bellingham ya yi fice a ƙungiyar Dortmund inda, a cikin watan Oktoban bara, ya kafa tarihi bayan ya zama kaftin ɗin kulob mafi ƙuruciya yana ɗan shekara 19.

Ya buga wa ƙungiyar wasa 42 daga shekara ta 2022 – 23, inda ya ci ƙwallo 14 kuma ya ba da ƙwallo bakwai aka zura a raga.

“Mun gode wa Jude saboda ƙwazonsa a tsawon shekara uku ga Borussia Dortmund. lokaci ne mai cike da burgewa,” babban jami’in Dortmund Hans-Joachim Watzke ya ce.

“Muna kuma so mu gode wa Real Madrid saboda tattaunawarsu mai cike da fa’ida da adalci a ko yaushe.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here