‘Yan bindiga sun yi garkuwa da daliban jami’ar Jos 7

0
111

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da safiyar ranar Laraba suka yi garkuwa da daliban jami’ar Jos (UNIJOS) su bakwai.

Wakilinmu ya nakalto cewa, lamarin ya faru ne da karfe 1:00 na safiya a gidan da daliban suke zaman haya a kusa tsohon makarantar koyar da ilimin Akanta (NSA) da ke kan hanyar Bauchi rod a cikin karamar hukumar Jos ta arewa, yayin da daliban ke tsaka da karatu domin zana jarabawar zango na biyu da suke kan yi.

Kazalika, an labarto cewa, ‘yan bindigan wadanda suka zo da yawa sun mamayi dakunan kwanan daliban inda suka fasa kofar shiga gidan tare da tilasta wa daliban shiga motarsu.

A lokacin da aka tuntubi Kakakin hukumar ‘yansandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, tunin aka tura jami’an hukumar domin su shiga daji domin ceto daliban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here