Har yanzu ba mu dauki mataki akan sababbin masarautu ba – Gwamnatin Kano

0
118

Gwamnatin jihar Kano ta karyata rade-radin da ake cewa zata dauki mataki akan sababbin masarautu.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar yace, har yanzu babu wani mataki da gwamnati ta dauka akansu.

Bature ya ce, ba zasu boye duk wani abu ba tsakanin bangaren gwamnati da majalisa ba domin bawa al’ummar jihar Kano damar sanin abinda yake faruwa akan matakan da gwamnati take dauka.

Da safiyar ranar Talata ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya tura sunayen mutum 20 da yake neman majalisar dokokin jihar su amince masa ya nada su a matsayin masu bashi shawara kuma tuni majisar ta amince a zaman da tayi na farko tun bayan rantsar da shugabanninta.

Ana saran a sati mai zuwa gwamnan jihar Kano zai tura sunayen kwamishinoni zuwa majalisa domin tantancewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here