Abba gida-gida ya dakatar da shugaban kwalejin lafiya da na makarantun sakandire na Kano

0
117

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da Shugaban Kwalejin Lafiya ta Health Technology, Bello Ɗalhatu, da Mai riƙon Shugabancin Hukumar Lura da Makarantun Sakandire ta jihar KSSMB, Malam Ado Tumfafi.

Hakan na cikin wata sanarwa da ofishin Sakataren Gwamnatin Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya fitar.

Freedom ta ce, sanarwar ta bayyana cewa an dakatar da su ne saboda zargin karɓar kuɗaɗe daga ɗalibai da kuma wasu ƙarin zarge-zarge.

Sanarwar ta zargi Tumfafi da karɓar kuɗin ɗalibai da sanya wa malamai harajin ba gaira ba dalili da sunan kuɗin fom ɗin ƙarin girma da sauransu.

Gwamnatin ta kuma umarci manyan sakatarorin ma’aikatun ilimi da lafiya da su kafa kwamitin bincike a kan mutane biyun.

Gwamnatin Kano ta ce ba zata sassauta wa duk wani shugaban hukuma da ya yi amfani da ofishinsa wajen cuzgunawa jama’a ba.

Haka kuma ta yi alƙawarin ƙwato wa iyayen ɗalibai da Malaman da aka karɓi kuɗaɗansu haƙƙoƙinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here