Bayern Munich na duba yiwuwar daukar Kyle Walker

0
145

Zakarun gasar Bundesliga na bana Bayern Munich na Duba yiwuwar daukar dan wasan baya na Manchester City Kyle Walker.

Walker wanda ya zo City a shekarar 2017 daga Tottenham Hostpur bai samu damar buga wasan karshe na gasar kofin zakarun Turai wanda kungiyarsa ta lashe bayan lallasa Inter Milan a filin wasa na Ataturk dake kasar Turkiyya.

Hakan na nufin Walker baya cikin Yan wasan da koci Pep Guardiola ke shirin tunkarar kakar badi, Mai shekaru 33 na cikin yan wasanda da Bayern Munich ke sa Ido akansu domin kara karfafa kungiyar.

Walker ya lashe kofuna da dama ciki har da gasar Firimiya 5, kofin kalubale 2 da kuma gasar zakarun Turai a shekaru 6 da ya shafe a Etihad bayan zuwansa daga Tottenham akan Yuro Miliyan 50 a 2017.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here