Wace illa manhajar GB WhatsApp ke da shi? Wannan ita ce tambayar da ake ta yi min a kwanan nan, sakamakon yadda mutane suke ta sanarwa cewa, duk wanda yake amfani da GB Whatsapp ya yi gaggawar goge shi.
Mutane da yawa suna amfani da GBWhatsapp ne, saboda yana da wasu tsarurruka da ‘Whatsapp’ na asali ba shi da su, kamar irin su adana (sabing) na hoto, bidiyo, ko kuma kwafin rubutu daga ‘status(es)’ na mutane kai tsaye, ko boye alamar karantawa ko karbar sako, ko don yana nuna alamar in mutum yana online, ko don tura ‘file’ mai nauyi, ko boye groups/chats, ko rubuta sunan ‘group’ da harafai sama da 35, yin status da harufai 250, a takaice. GBWhatsapp yana da wasu ‘features’ da normal whatsapp ba shi da su.
Amma, yana da kyau mutum ya sani cewa duk wadannan tarko ne na masu kutse ko madatsa ‘hackers’. Sun tsara shi ne ta yadda zai ba ka sha’awa sosai, fiye da manhajar WhatsApp na asali (normal Whatsapp), tare da ba ka damar wasan buya da ma’abota amfani da normal Whatsapp, musamma ma mata. Ka tura sako, a karanta, amma ba za ka ga alamar an karanta ba, sannan a duba status dinka ba tare da ka ga wanda ya gani ba.
To dai maganar gaskiya, kai tsaye, GBWhatsapp, ‘mod’ ne, ma’ana ba asalin Whatsapp ba ne. Asali an kirkire shi da ‘code’ (tsari) irin an Whatsapp na gaskiya, ba tare da samun lasisi daga kamfanin ba. Ina shawartar masu amfani da GBWhatsapp, da masu sha’awar amfani da shi, da su kauracewa manhajar saboda wadannan dalilai; shi GBWhatsapp ba sahihi ba ne daga asalin kamfanin Whatsapp, ‘AledMods’ ne suka yi shi, ba su da lasisi, kuma sun karya ka’idar kirkirar da ba da lamunin amfani da sirrikan jama’a. Shi ya sa ba za ka samu manhajar a Google Playstore (apk) ko AppStore (iOS, na Apple) ba. Kai! Ka ma taba ganin wani adireshi na yanar gizo na GBWhatsapp? Amsa babu, saboda ba su da gaskiya.