A makon da muka yi bankwana da shi ne kuma aka sake wayar gari ana ta ce-ce-ku-ce a kan jaruma Rahama Sadau.
Lamarin ya biyo bayan wani faifan bidiyonta ne da aka gan ta a ciki tana cewa a kashe karatun Alkur’ani a cikin motarta a sa mata waka.
Aminiya ta bi diddigin bidiyon, inda ta gano cewa lamarin ya faru ne a cikin fim din Nadiya na jarumar, inda ta fito a matsayin matar Umar M. Shareef.
A cikin fim din, jarumar ta fito a matsayin ’yar Rabi’u Rikadawa wanda ya fito a matsayin mai dukiya sosai ya shagwaba ’yarsa wato Rahama a fim din.
Wannan ya sa ta yi aure, amma ko wankan janaba da Sallah ba ta iya ba, sannan ba ta iya girka abinci ba, inda har ta kunya ta angonta a gaban abokansa da ya gayyata domin su ci abinci matarsa wayayya, amma suka kasa cin abincin saboda rashin dadinsa.
Daidai wajen da ya jawo magana, a daidai minti na 26 ne na fim din, jarumar ta fita a mota tare da direbanta mai suna Habu, inda a cikin motar yake sauraron karatun Alkur’ani, sai ta ce ya cire ya sa mata waka.
Da ya tambaye ta ta fi son wakar a kan karatun, sai ta ce, “Ban sani ba, kuma ban damu ba,” cikin harshen Ingilishi.
A wani faifan bidiyo da Sheikh Muhammad Auwal Maishago Zariya ya yada na wani malami, ya rubuta cewa, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Allah mun tuba, Allah kada ka kama mu da laifin da wawayen cikinmu suke aikatawa. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!”
A cikin bidiyon, malamin ya ce, “Hasbunallahu wa ni’imal wakil. Kun dai kalli bidiyon da ke kusa da ni da ’yar fim din Hausa mai suna Rahama Sadau ta yi, inda ta ce a cire Kur’ani a saka mata kida kuma ta yi tsaki kuma aka yi bidiyo aka yada saboda rashin kunya da rashin ladabi.
“To wallahi ita wannan ’yar fim Rahama Sadau muna jan hankalinta, ta yi gaggawar nadama ta koma zuwa ga Allah ta yi kuka ta yi takaici ta nemi Ya yafe mata.
“Idan ba haka ba, to wallahi ana jiye mata bala’i da wata masifa da za su iya riskarta tun a nan duniya saboda Kur’ani ba a yi masa rashin ladabi a kai labari.”
Da take mayar da martani a kasan rubutun, jarumar ta rubuta cewa, “Alaramma ai da ka kalli duka fim din kafin ka yi raddi a kai. Maganarka akwai rashin adalci a ciki.”
Shi kuma wani mai suna Sulaiman Iyali, wanda da alama masoyin jarumar ce, sai ya yi mata martani da cewa, “Tawa gaskiya, ya kamata mu tsaya a inda aka umarce mu da kuma inda aka hane mu. Domin addini da Alkur’ani ba ababen wasa ba ne. Allah (SWT) Ya sa mu dace.”
Wani mai suna Auwal Parruk ya ce, “Rahama Sadau maganarki haka take amma shawarata a matsayinki ta Musulma kuma mai kishin Musulunci ba kowace rawa za a baki ki hau ba, domin kuwa akwai abin da idan kika yi shi kin san dole a zarge ki kuma a matsayinki na Musulma addini ma bai yaddar ki rika yin abin da dole zai zama abin zargi gare ki ba. Allah Ya sa mu dace duniya da Lahira, amin.”
Mutane da dama da suka kalli fim din na Nadiya sun yi ta magana cewa fim ne ba zahiri ba domin kariya ga jarumar, sai wasu suka dira a kansu da zagi.
Wani mai suna Ibrahim Bin-baks ya rubuta cewa, “Allah Ubangiji Ya tsine wa masu cewa fim ne. Kur’ani shi ne abin wasa? Allah kuma Ya sa Kur’ani ya juya muku baya duniya da Lahira. Fasikan banza da wofi.”
Aminiya ta ruwaito yadda Rahama Sadau ta taba sa wasu hotuna da suka bayyana bayanta, wadanda a kasan hotunan wani ya yi batanci ga Manzon Allah (SAW), da hakan ya haifar da ce-ceku-ce mai zafi har mutanen Kannywood suka dakatar da ita kafin daga bisa ta bayar da hakuri ta nemi afuwa.
A watan jiya jarumar ta sake haifar da ce-ce-ku-ce a wajen taron karrama ’yan fim da aka yi a Legas, inda aka yi mata ca kan shigar da ta yi.