An bukaci musulman Najeriya su fara duban watan babban sallah yau Lahadi

0
133

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya umarci Musulmai a faɗin Nijeriya da su fara duban watan Dhul-Hijja na shekrar 1444 ta hijira daga yau Lahadi.

BBC ta rawaito cewa, cikin wata sanarwa da kwamitin duban wata na ƙasar ya fitar mai ɗauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu ta ce Sarkin Musulmin ya bayar da wannan umarni ne a ranar Asabar.

Sanarwar ta ƙara da cewa watan Dhul Hijja na da muhimmanci kamar sauran watannin Musulunci, kuma shi ne na 12 cikin jerin watanni kal, wanda a cikinsa ake yin ibadar aikin Hajji, tare da bikin Salla Babba.

“Muna san sanar da duka Musulmi cewa ranar Lahadi 18 ga watan Yuni ita ce ta yi daidai da 29 ga watan Dhul Ƙa’ada, ita ce kuma ranar da ya kamata a fara neman watan Dhul Hijja cikinta na hijira ta 1444.” in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here