An ceto daliban jami’ar Jos 6 da aka yi garkuwa da su

0
95

Rundunar ’yan sandan jihar Filato, ta ceto daliban jami’ar Jos guda 6 daga cikin guda 7 da aka yi garkuwa da su a daren ranar Litinin da ta gabata.

Kakakin rundunar, DSP Alfred Alabo ne ya bayyana haka a wata sanarwar da ya fitar a garin Jos, babban birnin Jihar Filato.

Ya ce rundunar ’yan sandan ta ceto dalibai guda 5, a yayin da dalibi ya tsere da kansa daga hanun masu garkuwar a wajen da suka boye su.

“Muna sanar da al’umma cewa a halin yanzu daliba 6 daga cikin 7 da aka yi, garkuwa da su, sun kubuta daga hanun masu garkuwa da mutanen.

“Kuma wannan ya faru ne sakamakon matakin da Kwamishinan ’yan sandan Jihar ta Filato, Bartholomew Onyeka ya dauka cikin gaggawa bayan faruwar al’amarin tare da hadin kan iyayen daliban.”

Aminiya ta ruwaito cewa, a daren ranar Litinin da ta gabata ne mahara suka yi awon gaba daliban, a lokacin da daliban ke tsaka da karatun zana jarrabawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here