An tsinci jariri a kusa da kango a Kaduna

0
126

An tsinci wani jariri sabuwar haihuwa a lullube da zani a kusa da wani kango da ke Unguwar Mu’azu a jihar Kaduna, a ranar Asabar.

Wani mutum ne dai ya tsinci jaririn wanda kuma daga bisani ya mika shi ga ’yan Kungiyar Sintirin ta Jihar, watau KADVs.

Jaririn dai an tsinci shi ne babu ko riga a jikinsa sai famfas da aka saka masa.

Sai dai ba a san wanda ya ajiye shi ba, ko kuma lokacin da aka kai shi wajen.

Wani jami’i wanda wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “A kusa da wani kango muka tsince shi, amma yana cikin koshin lafiya kuma tuni mun sanar da ofishin ’yan sandan Kabala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here