‘Yan Najeriya miliyan 71 na fama da bakin talauci – Rahoto

0
98

Wata sabuwar kididdiga ta duniya ta bayyana cewa, kimanin ‘yan Najeriya miliyan 71 na fama da bakin talauci, yayin da aka bayyana jihar Yobe a matsayin wadda ta fi fama da yunwa a kasar.

Tonye Cole, dan takarar gwamnan jihar Rivers karkashin jam’iyyar APC da ya gabatar da makala a wani taron ranar tunawa da yaki da yunwa ta duniya a birnin Abuja, ya bayyana cewa, wasu alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun ce, mutane dubu 25 ne ke mutuwa a kowacce rana sakamakon yunwa da suka hada da kananan yara dubu 10 a duniya.

Cole ya kuma bayyana cewa, Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta kiyasta mutane miliyan 133 da ke fama da nau’uka daban-daban na yunwa a kasar.

Ya ce, ya zama dole Najeriya ta dauki mataki domin tunkarar wannan matsalar ta bakin talauci a Najeriya.

Kwararru sun ce akwai wasu dalilai da ke haddasa talauci a Najeriya kamar rikice-rikice da gurbatacciyar gwamnati da rashin ingancin tsarin kiwon lafiya da suka ce ya zama dole a magance su cikin gaggawa muddin ana son kawar da yunwa a kasar.

Jihar Yobe ce ta fi fama da matsalar yunwa a Najeriya, inda take da kashi 44.2, sannan jihar ce ke kan gaba taa fuskar samun matsalar rashin abinci mai gina jiki, inda a wannan bangaren take da maki 27.4 kamar yadda masana suka bayyana.

Sai kuma jihohin Zamfara da Kebbi da Jigawa da ke biye da Yobe wajen samun wannan matsalar ta fatara da yunwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here