Zafi ya kashe mutum 100 a Arewacin Indiya

0
132

Hukumomi a Arewacin India sun ce cikin kwanakin da suka wuce an samu mutuwar mutane sama da 100 saboda matsanancin zafi da ake fama da shi a yankin.

Yanayin zafin ya haura digiri 40 a ma’aunin salshiyos a wasu yankunan Uttar Pradesh da Bihar.

Likitoci sun ce waÉ—anda suka mutun yawancinsu suna da wasu cutukan da ke da munsu dama, amma matsanancin zafin shi ne babban abin da ya janyo mutuwar tasu.

An kwantar da mutane sama da 400 a faÉ—in jihohin biyu sakamakon haka.

Ana ta bai wa dattijan da ke fama da wasu cutukan na daban shawarar su yi zamansu a gida.

Zafin ya jano Æ™arancin wuta lalacewar fankoki da na’urar sanyaya É—akuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here