Zulaihat Dikko Radda tayi kira ga Sanotoci da Yan Majalisun Katsina dasu jajirce wajen inganta kiwon lafiya a jihar

0
200

Hajiya Zulaihat Dikko Radda tayi kira ga yan Majalisu da Sanatoci na jihar Katsina da su maida hankali wajen inganta fannin lafiya a jihar.

Kiran ya biyo baya ne a yayin gudanar da walima wanda mutanen Musawa Matazu suka shirya ma Dan Majalisa mai wakiltar kananan hukumomin biyu Talban Musawa. A yayin jawabin nata Hajiya Zulaihat ta mika sakon godiya da bangajiya ga daukacin al’umar da suka halarci taron.

A yayin jawabin nata, mai dakin gwamnan kuma first lady ta jihar Katsina ta kara da cewa ” bincike ya nuna cewa jihar katsina ce tafi kowa ce jiha samun mata masu mutuwa yayin haihuwa”. Hakan ya biyo bayane sakamakon rashin samun ingantattun kayan aiki a mafi yawoan asibitoci. Tace yin hakan zaisa a samu raguwa na mace mace da mata da keyi kullum yayin haihuwa. Ta Kuma yi alkawarin tallafawa a wannen bangare.

Daga bisani ta kara jaddada ma al’umar Musawa da Matazu cewa mai girma gwamna yana sane da halin da al’umar jihar katsina suke ciki. A koda yaushe tunanin sa shine al’umar jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here