Abun da za ku so sani game da sabon mai rikon shugaban ‘yansanda Egbetokun

0
155

A daren ranar Litinin din nan ne shugaban kasa, Bola Tinubu, ya nada mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya DIG Kayode Egbetokun, a matsayin mukaddashin babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya gabanin majalisar dattawat a tabbatar da shi.

Har zuwa nadin nasa na baya-bayan nan, Egbetokun an ba shi mukamin Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda kuma mai kula da shiyyar Kudu-maso-Yamma a matsayin mai kula da sashen binciken manyan laifuka (FCID) a hedkwatar rundunar ’Yansanda da ke Abuja tun ranar 6 ga Afrilu, 2023.

An haifi sabon shugaban ’Yansandan ne a ranar 4 ga Satumba, 1964 a Erinja, karamar hukumar Yewa ta Kudu a Jihar Ogun kuma ya shiga aikin ‘Yansandan Nijeriya a ranar 3 ga Maris, 1990, a matsayin Mataimakin Sufeto na ‘Yansanda na sashen Cadet.

Ya samu horo na farko a makarantar ‘Yansanda ta Nijeriya, kuma ya halarci kwasa-kwasai da dama a ciki da wajen rundunar ‘Yansanda.

Ya yi aiki a wasu rundunonin ‘Yansanda da a fadin kasar nan, kuma ya rike mukaman kwamanda a lokuta daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here