Tinubu ya kori shugaban ‘yan sanda da na kwastam, ya nada sababbi

0
111

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron Kasa ba Babba Sufeton ’Yan Sanda da kuma shugaban Hukumar Kwastam ta Kasa.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar  ranar Litinin.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya raba wa manema labarai ciki har da sashen Hausa na Radio France International.

Sanarwar ta bayyana Manjo Janar C.G Musa a matsayin shugaban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, sai kuma Manjo T.A Lagbaja a matsayin shugaban sojin kasa, yayin da aka ayyana Rear Admiral E.A Ogalla a matsayin wanda zai jagoranci sojojin ruwan kasar, inda kuma AVM H.B Abubakar ke a matsayin sabon shugaban sojin sama.

Mataimakin Sufeta Janar na kasar, Kayode Egbetokun, shi aka ayyana a matsayin Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya na rikon kwarya.

Kazalika shugaba Tinubu ya amince da nadin Adeniyi Bashir Adewale a matsayin shugaban hukumar Kwastam na rikon kwarya.

Sanarwar ta ce, sabbin hafsoshin tsaron Najeriyar da Sufeta Janar na ‘yan sandan na rikon kwarya har ma da sabon shugaban na Kwastam za su ci gaba da gudanar da ayyukansu kafin lokacin da za a tabbatar da nadin nasu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

 

Kazalika shugaba Tinubu ya nada Nuhu Ribadu a matsayin mashawarcinsa kan al’amurran tsaron kasa, yayin da ya nada Hadiza Bala Usman a matsayin mai ba shi shawara ta musamman kan tsare-tsare.

Akwai sauran nade-nade da sabon shugaban na Najeriya ya yi a bangarori da dama a daidai lokacin da ‘yan kasar suka zura masa ido domin ganin yadda zai jagorance su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here